Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’amurra Sun Fara Daidaituwa a Garuruwan Dake Yankin Tafkin Chadi


Mata cikin kasuwar Kukawa

Al’amurra sun fara daidaituwa a gururuwan da aka kwato daga hannun kungiyar Boko Haram a yankin tafkin Chadi inda harkokin kasuwanci suka kankama a Karamar Hukumar mulki ta Kukawa dake jihar Borno

Al’amurra sun fara daidaituwa a garuruwan dake yankin tafkin Chadi da aka kwato daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Yanzu haka harkokin kasuwanci sun kankama a karamar hukumar Kukawa dake cikin jihar Borno, karamar hukumar da ta yi fice wajen kasuwanci daban daban. Bugu da kari, dubun dubatan mutane ne suka koma gidajensu yayinda wasu kuma suke shirin komawa daga sansanin da suke yanzu.

Wakilin Muryar Amurka dake jihar Borno, Haruna Dauda, ya ziyarci garin Kukawa har ma ya kwana a garin inda ya lura jami’an tsaro na ci gaba da yin sintiri domin samar da tsaro da kariya ga al’umman garin.

Samun zaman lafiya a garin ya sa har mutanen sun soma tunawa da al’adunsu. Ana jin kade kade a cikin dare, alamar cewa akwai kwanciyar hankali.

A cikin kasuwar garin Kukawan Haruna Dauda ya ga mutane suna hada-hadar kasuwanci ya kuma zanta da wasu daga cikinsu, inda suka yiwa Allah godiya, koda yake wasunsu sun ce har yanzu suna fuskantar wasu matsalolin muhalli da kayan abinci da suke son gwamnan ya taimake su a kansu.

Gwamnan jihar ta Borno, Kashim Shettima, da kansa ya kai ziyara gani da idanunsa a garin inda kuma ake zantawa akan yadda za’a yi da taimakon da suka samu daga shugaban kasa, Muhammad Buhari.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG