Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'amura Sun Fara Farfadowa A Birnin Mogadishu


Bankin Dahabshil a birnin Mogadishu kasar Somalia

'Yan kasuwa sun fara yin tururuwa su na zuwa birnin Mogadishu

A dai dai lokaci da aka fara ganin birnin Mogadishun Somalia ya fara farfadowa gadan-gadan daga yakin basasar da aka dauki shekara-da shekaru ana fafatawa, yanzu kuma ‘yan kasuwa da masu zuba jari sai tumbudi suke yi zuwa birnin, haka suma ‘yan kasar da suka yi hijira zuwa kasar waje domin kaucewa yakin basasar. A rahoton da wakilin Muryar Amurka Gabe Joselow ya aiko daga birnin Mogadishu, yayi bayanin cewa ganin yadda ake ruwan kudaden agaji daga kasa da kasa, an fara ganin ‘yan kasuwa na kokarin bubbude sabbin Masana’atun cinikayya a sassa dabam-dabam na birnin Mogadishu.

Liban Mahdi na daga cikin ‘yan kasar da suka yi gudun hijira kuma yanzu ya koma domin kokarta yin amfanio da damar da aka samu ta gina kananan masana’antu bayan da ya shafe shekaru 25 yana zaune a kasashen Canada da Amurka yanzu kuma ya koma birnin Mogadishu inda ya sami aikin farfgado da gagarumin Otel-din na Makkah Hotel.

Shi wannan gagarumin Otel din, anyi kaca-kaca dashi ne a a lokacin yakin basasa. Anji yana fada da bakinsa cewa shi da ‘yanuwansa da suka mallaki wajen ne suka hada karfinsu waje guda domin sake farafdo da Otel din domin samun ayyukan yi bayan gudun hijira.Idan za’a tunawa, yace a watan Maris da ya gabata ne ya fara da bude wani katafaren shagon saida Kofin irin na kasar Kenya, wanda ke jingine da wani baban gidan saida abinchi. Shagon nasa kuma a cike yake da kayan abinchi karya kumallo iri dabam-daban da fanke, da kek da kosan turawa, sannan kuma wajen sai ya zama matattara da shirya tarukan jama’a inda mafi yawan ‘yan kasar Kenya dake daowawa daga gudun hijira ke haduwa domin tuna baya.
XS
SM
MD
LG