Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Abu Dankure Ya Rasu Kwanaki 10 Bayan Sako Shi


An baza jami'an tsaro a muhimman wurare a Nijeriya amma har yazu batagari na aika-aika.
An baza jami'an tsaro a muhimman wurare a Nijeriya amma har yazu batagari na aika-aika.

Hamshakin dankasuwa kuma shaharraren dan siyasar nan na Sakkwato da wasu miyagu su ka sace shi kwanan baya mai suna Alhaji Abu Dankure ya rasu da asubahin yau.

Hamshakin dankasuwa kuma shaharraren dan siyasar nan na jihar Sakkwato da wasu miyagu su ka sace shi kwanan baya mai suna Alhaji Abu Dankure ya rasu da asubahin yau, wato bayan kwanaki 10 kenan da sako shi daga sace shi din da aka yi ranar 6 ga wannan wata.

Dinbin jama’a ne su ka halarci jana’izar mamacin ciki har da Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko da Mataimakinsa Muktari Aliyu Shagari da sauran masu fada a ji da dama.

Wakilinmu na Sakkwato da ya aiko da rahoton wato Murtala Faruk Sanyinna ya yi hira da daya daga cikin wadanda su ka yi ma mamacin kallon karshe mai suna Auwal Ila, wanda ya ce jiya da ya je gidan ya bukaci ganin Alhaji Kure, wanda ya ce a matsayin uba ya ke gare shi saboda kanin Ubansa ne, sai aka ce masa Alhaji Dankuren baya da lafiya. Ya ce a asibiti Alhaji Dankure ya rasu. Da ya ke amsa tambayar wakilinmu Ila ya ce al’amarin bai rasa nasaba da sace shi da aka yi kwanan nan saboda likitoci ma sun ce bugun zuciya ne.

Wakilin mu ya jaddada cewa tun lokacin da aka sako Alhaji Dankure ya ke fama da rashin lafiya. To saidai a lokacin da alamar bai yi tsanani ba. Hasalima Murtala ya ruwaito shi ya na ta godiya ga Allah da jama’a saboda sakin nasa har ya na cewa miyagun basu kuntata masa ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG