Yayin da ake haramar dawowa daga aikin Hajjin bana, Alhazan Najeriya dake Mina suna fuskantar matsalolin wurin kwana da kuma wurin kewayawa.
Wannan yasa wasu da yawa suke kwana waje, yayinda wasu da yawa kuma sai sun shiga dogon layi kafin su samu damar kewaya wa.
Wannan lamarin ya fito fili ne lokacin da shugaban hukumar Alhazan Najeriya Barister Abdullahi Mukthar Mohammed ya zagaya wurin kwanan Alhazan domin ganin halin da suke ciki.
Jihohin da abin yafi shafa sun hada da Kaduna, Kano, Sokoto da Bauchi.
Imam Hussaini Tsoho shine shugaban Alhazan jihar Kaduna kuma ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya cewa, wasu Alhazan ma basu da ko katifan kwanciya sai sun dauko dardumar da aka shinfida cikin tanti sun fito waje sun shinfida.
Haka kuma Imam Tsoho yayi korafi gameda bukatar samarda makewayin mata daban, na maza dadan.
Ga Nasir Adamu El-Hikaya da karin Bayani: 2’48
Facebook Forum