Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alka’ida Da Da’esh Na Aikin Kirkirar Wasu Nau'in Makamai


Kafofin yada labarai a Amurka sunce kungiyoyin tsageru na kera nau’rar bam wacce za’a iya boyeta a cikin karamar nau’ra mai kwakwalwa wacce za’a iya wucewa da ita batare da wasu daga cikin jami’an tsaron tashohin jiragen sama sun ganeba.

Kafafen yada labarai na CNN da CBS sun ce jami’an tsaron Amurka sun fada musu cewar ‘Yan tsagerun Alka’ida dana Da’esh suna aikin kirkirar hanyoyin kera wannan makami a cikin naurori masu amfani da lantarki.

Kafafen yada labaran sun kara da cewa ‘Yan tsagerun sun sami manyan kayan bincike na tsaron tashoshin jiragen sama don yin gwajin yadda zasu iya wucewa da nakiyar cikin jirgi kai tsaye.

Sunce bayanin ya taka rawa wajen hukuncin da gwamnatin Trump ta yanke na hana matafiya masu tashi daga filayen jirgin sama 10 a kasashe 8 na gabas ta tsakiya da kuma Afirka daukar karamar na’ura mai kwakwalwa da sau ran nau’rori masu amfani da lantarki shiga dasu cikin jirgi inda fasinjoji ke zama.

A farkon wannan watan ne gwamnatin Amurka ta haramta shiga da Karamar na’ura mai kwakwalwa, ciki harda na’urar Ipads da Na’urar Daukan Hoto cikin jirgi inda fasinja ke zama yayin shiga Amurka daga tashoshin jiragen sama 10 da suka hada da kasar Misra, da Jordan da Kuwait da Morocco da Qatar da Saudi Arabiya da Turkiya da kuma daular larabawa wato UAE. Kasar Birtaniya itama ta dauki irin wannan matakin.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG