Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalan Somalia Sun Yi Watsi da Sakamakon Zaben Majalisa


Wata mata tana jefa kuri'a a zaben da alkalai suka yi watsi da sakamakonsa
Wata mata tana jefa kuri'a a zaben da alkalai suka yi watsi da sakamakonsa

Soke sakamakon zaben da aka yi a Somalia da alkalan kasar suka yi watsi dashi ka iya zama alakakai ga zaben shugaban kasa da aka shirya yi a karshen wannan shekara

A Somalia kuma, kwamitin alkalai da suka yi shari’a a kan takaddamar zabe sun yi watsi da sakamakon zabukan kujerun majalisu goma sha daya sanadiyar kurakurai da aka gano har da harbin bindiga da aka yi a wata runfar zabe.

Hukunci da kwamitin alkalai masu shari’a a kan lamurran zabe a Somalia, zai iya kawowa zaben shugaban kasa cikas da kasar ke niyar yi a karshen shekara.

Masu sukar lamirin kwamitin sun ce akwai wasu muhimman batutuwan magudin zabe da ba a kula da su ba. Suka ce a cikin batutuwan akwai tsoma baki kai tsaye daga fadar shugaban kasa Hassan Sheikh Mohamoud.

Sai dai shugaba Mohamoud bai mai da martani a kan wannan zargi ba.

XS
SM
MD
LG