Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalin Alkalan Najeriya Ya Damu Da Jinkiri Wajen Yanke Hukunci.


Alkalin Alkalan Najeriya Chief Justice Onnoghen
Alkalin Alkalan Najeriya Chief Justice Onnoghen

A taron alakalan Najeriya da aka fara a Abuja alkalin alkalan Najeriya Cif Joji Onnoghen, ya bara da gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kotuna tare da rashin yanke hukumci cikin gaggawa

Yayinda yake bude taron alkalai a Abuja, alkalin alkalan Najeriya, Cif joji Wilson Onnoghen, ya nuna damuwarsa kan gibin dake akwai tsakanin manya da kananan kutuna, musamman a matakan jihohi.

Inji alkalin alkalan gibin dake tsakaninsu shi ne sanadiyar rauni da ana kotunan suke fama dashi. Mai Shari'a Onnoghen ya ce idan ana son cimma nasara, dole ne a cike gibin dake akwai musamman akan 'yancin cin gashin kai, da samar da kayan aiki da ma kudade a fannin shari'a a matakan jihohi.

Kazalika alkalin alkalan ya bara akan jinkirin da ake samu wajen yanke hukumci a shari'un kasar. Injishi wannan jinkirin da ake samu babban damuwa ne a gare shi. Yana gani yakamata ya zama abun damuwa ga alkalan kuma lamari ne da bai kamata a amince dashi ba. A cewar sa akwai bukatar sake duba kundin tsarin shari'ar kasar.

Wani lauya mai zaman kansa a Abuja Barrister Modibo Bakari, ya ce dole Alkalin Alkalai ya yi magana akan lamarin idan bai yi ba, da za'a yi mamaki saboda akwai doka da ta ce a gaggauta yanke hukumci, amma kawo yanzu babu tsawatar wa da ake yiwa alkalan. Ya ce an bar alkalai kara zube sai abun da suka ga dama su keyi.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG