Accessibility links

Allah Wadai Da Harin Da Amurka Ta Kai Afghanistan : Hamid Karzai


Alkalluma na hauhawa na mutanen da suka mutu sanadiyar bam din nan mafi karfi da Amuka ta jefa a kasar Afghanistan.

Jami’ai a kasar Afghanistan sun ce adadin ‘yan tsagerun da suka mutu a sanadiyar kasurgumin Bam din nan mafi karfi da Amurka ta jefa a ranar Alhamis da ta gabata na kara hauhawa.

Jami’an sun bayyana cewa ya zuwa yanzu dai kimanin ‘Yan tsagerun 92 ne suka mutu a harin – wanda ya haura 36 da aka bada rahoto da fari a ranar juma’a. Har yanzu dai ana kan bincike a wurin, saboda haka yawan wadanda suka rasu zai iya karuwa.

Babu wata alama da tuna Fararen hula ko jami’an soji sun mutu a harin.

Shugaban kasar Afghamistan Ashraf Ghani yace Dakarun Amurka dana Afghanistan sun yi aiki tare wajen aiwatar da harin Bam din, amma tshohon shugaban kasar da ya gada yayi Allah wadai da wannan hari da Amurka takai.

Tsohon shugaban kasar ta Afghanistan Hamid Karzai ya fada a yau Asabar cewa zai kaddamar da Kamfe na baji ba gani domin tilasta wa dakarun Amurka su fita daga kasar sa sakamkon jefa wannan Bam da akewa lakabi da “Uwar Bama Bamai” akan kasar Afghanistan. Wanda ya kira da “Rashin Imani” don gwajin makamin kare dangi bawai don kaiwa mayakan ISIS hariba.

Fadar shugaban kasar Afghanistan ta maida martini ga tsohon shugaban kasar ta Afghanistan a shafin twitter inda aka rubuta “Kowanne dan kasar Afghanistan nada ‘yancin bayyana ra’ayinsa , Wannna kasace ta ‘Yancin Magana.”

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG