Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yi ma Sarkin Borgu, Alhaji Halliru Dantoro, Rasuwa


Wasu sarakai a jahar Naija

Jama'ar jahar Naija na makokin rashin daya daga cikin iyayen kasa, Mai Martaba Sarkin Borgu, Alhaji Halliru Dantoro

Sarkin Borgu Alhaji Halliru Dantoro (Na Uku), dan shekaru 78, ya rasu a wani asibitin kasar Jamus a jiya Jumma’a sanadiyya wani gajeran rashin lafiya. Wata sanarwar gwamnatin jahar, mai dauke sa hannun mai baiwa gwamnan jahar shawara kan harkokin jarida Mr Jide Oritusin, ta ce rasuwar sarkin babban rashi ne ga Najeriya baki daya.

Marigayin shi ne Shugaban Karamar Hukumar Borgu na farko. Ya kuma taba yin Kwamishina a tsohuwar jahar Kwara wadda yankin na Borgu ke ciki lokacin. Mai martaba Alhaji Halliru Dantoro ya taba yin Sanata da kuma Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja.

Daga cikin masu nuna juyayin rasuwar Sarkin na Borgu har da wazirin Borgu Alhaji Nuhu Sa’adu Abdullahi, wanda ya gaya ma wakilinmu a Neja Mustapha Nasiru Batsari cewa babu mai ja da ikon Allah, don haka Allah ya jikansa. Y ace marigayi adali ne mai tsaron Allah, son gaskiya da kuma rikon amana.

Ga Mustapha da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG