Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Almajirai Kimanin Miliyan Uku Ke Kano-Ganduje


Almajiran tsangaya dake koyaon karatun allo

A makon jiya ne, Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana a Kaduna cewa akwai kimanin almajirai miliyan uku a jihar Kano.

A cewar gwamnan galibin almajiran sun je jihar ne daga wasu jihohin arewa wasu kuma sun fito ne daga kasashen dake makwaftaka da jihar ko Najeriya.

Malam Ishak Zeru dake zama naibin limamin Masallacin Juma'a na Murtala a Kano yana da almajirai dake karatun allo a gidansa. Yana mai cewa sau tari sai a kwaso yara a ajiyewa malam ba tare da wani taimako ba. Wasu ma sun fito da yaransu ne daga wasu kasashe kafin a farga sai su gudu su barsu, ke nan a bar malamin da yaran.

Yace a duba duk wanda yake alamajiri nagari ba za'a ganshi a tituna ba ranar Asabar, Lahadi zuwa Litinin. Yace idan ana son tsarin ya tafi sosai 'yan'yan kuma su zama managarta, suga kimar karatu da kimar malamansu sai an koma tsari iri na wasu kasashe. Dole iyaye su dauki wasu nauyin abubuwan da zasu dinga yi kullum domin 'ya'yansu.

Dr Muhammad Hadi Musa masanin ilimin zamantakewar al'umma da lamuran iyali ne, ya kira gwamnatocin arewa su fito da tsarin magance matsalar gabanin su hana al'umma sakewa a shekaru masu zuwa.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG