Accessibility links

Al'mumar Fulani dake yankin Shandam, a jihar Filato sun koka abisa kisan yaran su biyar da kuma satan shanu.

A yamacin jiya ne ‘yan bindiga suka afkawa kauyen Dawur a karamar hukumar Shandam, inda suka kashe makiyaya biyar suka kuma kore masu shanu.

Ardon Shandam wanda kuma shine Sakataren kudi na kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato Malam. Dabo Jauro,yace a lokacin da yaransu suka fita kiwo a Yelwan Shandam sai ‘yan kabilan Tarok, suka farwa masu inda suka kashe mutane biyar suka kuma sace shanu dari biyu da ashirin.

Shi kuwa sakatare janar na ‘yan kabilan Tarok, Pastor, Nanlir Nabut, yace ba’a kama wadanda suka aikata wannan ta’asarba saboda haka ba dai-dai bane a ce ‘yan Tarok ne suka aikata.

XS
SM
MD
LG