Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Arewa Maso Gabas Sun Gudanar da Taro kan Sake Fasalin Najeriya


Taron sake fasalin Najeriya na al'ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya
Taron sake fasalin Najeriya na al'ummar Arewa Maso Gabashin Najeriya

A cigaba da muhawara kan sake fasalin Najeriya al'ummar arewa maso gabashin Najeriya sun yi taro a Bauchi inda suka tattauna suka bada tasu shawarar kan yadda ya kamata Najeriya ta kasance.

Mahalarta taron sun hada da 'yan siyasa, iyayen kasa, kungiyoyin kare hakkin 'yan kasa, kungiyoyin mata da matasa da dai sauransu.

Taron ya gayyato mutanen da suka yi magana kan sallon mulki, sabon lale da tsarin fitar da sabon mulki da irin hukuncin da ya kamata a aiwatar kan masu yiwa mata fyade da masu yiwa tattalin arzikin kasa aibu da harkokin 'yansanda.

Wadanda suka gabatar da kasidu sun yi karin bayani. Injiniya Sa'adu Abubakar Abdullahi da tawagarsa sun bada kasida akan tsarin mulkin yanzu na shugaban kasa mai cikakken ikko da majalisu biyu. Suna da ra'ayin cewa wannan shirin yana da tsada. Ana kashe kudi da yawa wajen gudanar dashi. Kamata yayi a koma irin na da mai firayim minista da shugaban kasa mai karamin iko. Shirin shi ne zai ba gwamnati isasshen kudin da za'a yiwa talaka aiki.

Wasu kuma sun gabatar da kasida akan maganar matasa da shugabanci, da kafa 'yansandan jiha da kuma ba jihohi mulkin arzikin jiharsu. Su dai ba sa son a baiwa jihohi ikon mallakar 'yansanda saboda wai ba zai haifar wa kasar da mai ido ba.

Wasu na kiran a tsare gaskiya. Suna mai cewa kada a kara ko a rage jihohi. A tsaya a 36 da kasar ke dasu yanzu saboda ko yanzu ma kimanin jihohi goma ne kawai ke iya biyan albashi a kan lokaci.

Mata ma ba'a barsu a baya ba. Sun bada kasida kan yawan fyade da ake yiwa mata yara kanana.Suna son duk wanda aka kama yayi fyade a yi masa daurin rai da rai.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG