Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Kiru da Bebeji dake Jihar Kano Sun Kai Majalisar Wakilan Najeriya Kara Kotu


ABUJA: Abdulmummuni Jibrin dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji, da majalisar ta dakatar
ABUJA: Abdulmummuni Jibrin dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji, da majalisar ta dakatar

Kwanakin baya ne lokacin rikicin cogen da aka ce 'yan majalisa sun yiwa kasafin kudin bana Abdulmummuni Jibrin ya fito ya zargi majalisa da yin magudi lamarin da ya sa suka dakatar dashi har na tsawon kwanaki 180

A karshen makon da ya gabata ne wasu mutane su 29 suka wakilci al'ummar kananan hukumomin Kiru da Bebeji wajen kai majalisar wakilan Najeriya kara kotu akan dakatar da mai wakiltarsu Onarebul Abdulmummuni Jibrin.

Barrister Muhammad Bashir Muntaka shi ne lauyan al'ummar. Yace mutanen da suka zabi Abdulmummuni Jibrin sun gaji da zama basu da wakilci a majalisar. Mutanen suna ganin dakatar da dan majalisar har na tsawon kwanaki 180 an sabawa ka'ida.Inji Barrister Muntaka babu wata doka da ta baiwa majalisar ikon dakatar da wani dan majalisar fiye da kwanaki 14. Babu wata doka da ta amince da kwanaki fiye da haka.

Hakazalika Barrister Muntaka ya fayyace abubuwan da al'ummar Kiru da Bebeji ke bukata daga kotun. Suna son kotun tace dakatarwar da aka yiwa Abulmummuni Jibrin bata kan ka'ida. Kotu kuma ta biyashi kadu da hakkin da aka tauye masa na kwanakin da aka dakatar dashi.

Abdullahi Bulama lauya dake Kano ya yaba da yunkurin mutanen. Yace abun da suka yi zai karawa dimokradiya armashi kuma zai ba na baya su san iyakar karfin majalisar.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

XS
SM
MD
LG