Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Kasar Nijar Sun Bayyana Ra'ayoyinsu Akan Zaben Amurka


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Zaben shugaban Amurka ba 'yan Amurka kadai suke sa ido ko suka damu dashi ba saboda a duniya ana ganin shugaban Amurka shugaban duniya ne.

Muryar Amurka ta zagaya Jamhuriyar Nijar domin jin ra'ayoyin jama'ar kasar akan zaben shugaban kasar Amurka da za'a gudanar gobe Talata idan Allah Ya kaimu.

Nasiru Seidu shugaban kungiyar talaka ta Nijar yace yana fatan amurkawa zasu zabi mutum wanda zai iya daukan nauyin kasar wanda kuma ya gane cewa yana da nauyin duniya a kansa. Saboda haka ya kirasu su yi rairaiye da tankada da tacewa kafin su jefa kuri'unsu. Ya kira su zabi shugaban kasa da ya dace da manufofinsu. Yana fata za'a zabi wanda ya san manufofin duniya saboda kasar tana da matsayi a duniya, wanda zai hada kan mutane tare da neman zaman lafiyar duniya.

Shi kuwa Alhaji Idi Abdu yace kasashen Afirka na rudan kansu ne kawai. Duk wanda aka zaba shugaban Amurka ne kuma babu abun mahimmanci da zai yiwa Afirka. Yace amurkawa sun banbanta da mutanen Afirka domin suna kishin kasarsu kuma sun san abun da suke so. Basa zabe bisa kabilanci ko bangaranci ko kudi kamar yadda ake yi a Afirka.

Akan 'yan takaran biyu Idi Abdu yace duk suna da tabo amma namijin ya fi razana mutanen kasar da ma na waje bisa wasu kalamunsa. Yace ba'a son shugaba mai kalamu irin na shi namijin.Duk duniya tana yin fargaba saboda shi bisa kalamunsa. Yana fata Amurka zata zabi nitsatse mai neman kwanciyar hankali.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG