Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummomin Arewa Maso Gabas na Zargin An Yi masu Coge a Wakilan Taron Kasa


Wasu wakilan taron kasa
Wasu wakilan taron kasa

Kodayake za'a fara taron kasa yau Litinin al'ummomin arewa maso gasa na zargin an yi masu coge a jerin sunayen wadanda zasu wakilcesu.

Yau Litinin za'a fara taron kasa a Najeriya amma sai dai al'ummomin arewa maso gabas sun koka da yadda aka sauya masu sunayen wakilan da suka zaba da wasu daban.

Mr. Joseph Gimba na cibiyar cigaban lafiya dake Jalingo jihar Taraba yace an sauya sunayen da suka bayar tun farko. Yace sun tara sunaye sun aika Abuja kana a ka ba sakataren gwamnati har ma sunayen sun fita a jaridar Thisday amma abun mamaki sai sunayen wasu daban suka fito. Yace wannan aikin 'yan Abuja ne. Abun da suke so shi ne a bi sunayen farko da suka zaba a dimokradiyance.

A jihar Yobe ma al'umma na irin wannan korafin inda Baba Shehu na kungiyar Yobe Network for Civil Society yace sun yi zabe sun zabi mutum daya daga Gombe, Yobe, Bauchi da Taraba sun kuma tura sunayen Abuja. Amma sunayen da suka bayar ba su ne suka fita ba. Gaba daya ma babu sunaye daga arewa maso gabas. Wato ma'ana basu da wakilci ke nan.

To har wayau wasu na shakku da taron. Rev Matthew Kukah na ganin akwai abun dubawa game da taron. Yace taron ba na damuwa da halin da talaka ke ciki bane domin 'yansiyasa da gwamnoni da shugaban kasa su ne zasu zabi mahalartan kuma irin yasu-yasu ne zasu zaba ba ainihin 'yan Najeriya ba dake cikin kuncin rayuwa. Tace duk wadanda basa so ba zasu samu su halarci taron ba. Abu na gaba shi ne 'yan siyasa zasu je Abuja su yi abun da suka saba yi. Yace za'a gama taron a watse amma ba'a yi komi a kan matsalolin kasar ba.

A wani gefen kuma mutane irin su Fidelis Tapgun tsohon gwamnan Filato gani yake taron ya dace a yishi domin yana da mahimmanci. Yace taron zai baiwa 'yan kasar dama su zauna su tattauna kan abubuwan dake damun al'ummar kasar. Yace tun lokacin da Lord Luggard ya hada Najeriya wasu ne suke yiwa kasar kundun tsarin mulki, amma yanzu 'yan kasar na da zarafin kirkiro da irin kundun tsarin mulkin da suke so. Abubuwa da yawa na faruwa a kasar kuma bai kamata su faru ba.

Ga cikakken rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG