Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 150 a Rasha


Ambaliyar ruwa a Rasha

Yawan mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a kudancin kasar Rasha, ya karu zuwa dari da hamsin, a yau Lahadi

Yau Lahadi yawan mutanen da aambaliyar ruwa ta kashe a Rasha ya karu zuwa dari da hamsin. A jiya asabar, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ziyarci yankin da ambaliyar ta yiwa barna a kudancin kasar ya kuma bada umarnin ayi bincike a ganin dada ko sakaci ko kuma tafiyar hawaniyar daukan mataki da jami’ai a Krasnodar suka yi ne kila, yasa har fiye da mutane dari da arba’in da hudu suka mutu.

Gidan talibijin na Rasha ya nuna shugaba Putin yana zantawa da jami’an ma’aikatar daukan matakan gaggawa wadanda suka tabbatar masa da cewa, ba madatsar ruwan dake kusa ne ta hadasa matsalar ambaliyar ruwa kamar yadda mazauna yankin suka yi zargi ba.

Ba’a yiwa mazauna garin Krymsk, garin da yafi dandanawa daga wannan masifa, kashedi kafin aukuwar ambaliyar ruwa da tsakar dare data sa gidaje da motoci yi iyo cikin ambaliya da lalata wasu wurare kuma ta cinye wasu mutane ba. Yawancin wadanda ambaliyar ta yiwa barna sunce har yanzu babu wani taimakon da aka basu.

XS
SM
MD
LG