Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna A Bauchi


Wasu da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Sudan

Mutane da dama sun sami raunuka banda asarar dukiyoyi na miliyoyin nairori sanadiyyar ambaliyar ruwa a Bauchi.

Wata mummunar ambaliyar ruwa ta yi sanadin jin raunuka da kuma asarar dukiyoyi a Bauchi. Tuni dai Gwamnan Bauchi Alhaji Isah Yuguda ya zagaya don gane wa kansa irin barnar da ta auku in ji wakilinmu na shiyyar Bauchi Abdulwahab Muhammad.

Bayan da ya gama zagayawa don ganin abin da ya faru, sai Gwamnai Isah Yuguda ya gaya wa 'yan jarida cewa ba a sami rasa rai ba amma an jijji ciwo banda asarar rayuka. Don haka ya jajanta wa mutanen jihar sannan ya yi kiran da a daina gine-gine kan hanyoyin malalar ruwa; a tsabtace muhallai sannan a kuma kauce wa yin gini a kwari da dai sauran abubuwan da kan sa a fuskanci ambaliyar ruwa.

Gwamna ya ce ambaliyar ta cika dakunan bahaya sun sun yi ta tunbudin ruwan najasa, wanda ya malala har cikin rijiyoyin jama'a. Don haka Gwamna Yuguda ya yi kira ga duk mai salga a gida ya rinka dafa ruwan sha; ya na mai alkawarin gwamnati za ta samar da sinadarin Chlorine na tsabtace ruwa ga duk mai bukata.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG