Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani da Matasa a Matsayin 'Yan Bangar Siyasa


Bangar Siyasa
Bangar Siyasa

Yayin da kungiyoyin siyasa suka dukufa wajen yakin neman zabe don tallata ‘yan takarar su, kuma su kansu ‘yan takarar ke kada gangar a zabe su koda ma basu ta buka komai ba a baya, Fulani makiyayya suma a wannan karon sun yunkuro a dama dasu.

Tuni Fulanin suka kafa sabuwar kungiyar siyasa, wanda Alhaji Usman Usman Fulani, kewa jagoranci, yace an kafa kungiyar ne domin kara wayarwa da Fulani kai, dangane da siyasa, da zamar lafiya.

Su kuwa a nasu bangaren jami’an tsaro sun dukufa ne wajen kunnen ‘yan siyasan dake amfani da matasa, a matsayin ‘yan bangan siyasa, DSP Usman Abubakar, kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Adamawa, yace amfani da ‘yan bangar siyasa bashi da wani afanu ga jama’a, ya kuma kara da cewa rundunar ta dauki kwararan matakai, na ganin cewa hakan bai faru ba.

Bangar siyasa - 3'24
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG