Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Kan Azumi-Afrilu, 24, 2022


Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalama alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.

Yau za a ji kashi na farko na amsoshin masu sauraronmu da daman gaske, kan abubuwan da su ka shafi azumi: Kamar fa’idojin azumin, abubuwan da ya kamata mai azumi ya dukufa wajen yi; mutanen da azumin ya wajaba kansu da kuma fa’idar goman karshe da dai sauransu.

To idan dinbin masu tambayoyin na tare da mu, Shugaban Majalisar Malaman Izala Shiyyar Birnin Tarayyar Najeriya, kuma Sarkin Malaman Duguri, Sheikh Muhammad Ibrahim Duguri yau zai gabatar da kashi na farko na amsoshin tambayoyin.

A kasance da mu makon gobe don jin kashi na biyu kuma na karshe na amsoshin tambayoyi kan azumi.

A saurari cikakken shirin na Amsoshin Tambayoyinku:

please wait

No media source currently available

0:00 0:12:19 0:00

Dubi ra’ayoyi

XS
SM
MD
LG