Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amsoshin Tambayoyinku: Tarihin Sheikh Albani Zaria


Ibrahim Ka-Almasih Garba
Ibrahim Ka-Almasih Garba

Rashin kuskure a hasasoshin da marigayi Sheikh Albani Zaria ya yi tun ya na raye, cewa idan Buhari ya dau matakan gyara Najeriya, to labudda wahala mai tsanani za ta gabaci duk wata nasarar da za a yi, ya sa an yi ta tambayar tarihinsa.

To tun bayan da aka shiga fama a Najeriya, sanadiyyar wasu dalilai, da su ka hada da matakan gyara da gwamnatin Najeriyar ta dauka, wasu da su ka tuna da hasashen da marigayi Shiekh Albani Zaria ya yi, kan yadda duk wata gyarar Najeriya za ta zo da wasu wahalhalun da ya zayyana dalla-dalla, su ka sake sakin wadannan faya fayen wa’azin nasa, ganin yadda bayanansa su ka zo daidai na abin da ke faruwa.

A daidai wannan lokacin masu sauraronmu da dama, sun shiga tambayar tarihin marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, wanda mahaifansa ‘yan asalin Kano ne, amma aka haife shi a unguwar Muchia, Zaria, wasu ‘yan bindiga kuma su ka kashe shi ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2014.

To dayake a lokacin da ‘yan bindigar su ka yi wannan danyen aikin, an yi irin wannan tambayar akai akai, ta bukatar tarihin Sheikh Albani, kuma wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isah Lawan Ikara, ya samo amsa daga daya daga cikin daliban marigayin Daraktan makarantar Salafiyya ta Sheikh Albani da ke Zariya, Dr. Adulrafiyu Abdulganiyu, mun sake gabatar ma masu tambayoyi a yanzu waccen amsar.

Ga cikakken shirin ta sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:13:21 0:00


XS
SM
MD
LG