Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
Tambaya:
Assalama alaikum Muryar Amurka. So na ke a yi min karin haske a kan wutar daji da ke aukuwa a wasu yankunan kasashen Turai:-
*Shin ko wannan wutar ta na da alaka da yanayin zafi da ake ciki?
*In har akwai alaka, to me ya sa wannan wutar ba a cika ganinta ba a kasashenmu na Afurka duk da yake cewa yanayin zafinmu ya fi na Turai?
Mai tambaya: Ado Turaki Askira, jihar Bornon Najeriya.
Amsar:
Idan Malam Ado Turaki Askira da ma sauran masu saurare na tare da mu, ga kashi na daya na amsar tambayarka game da gobarar dajin da aka fai yi a Turai. Wakilinmu a Adamawa, Muhammadu Salisu Garba, ya samo ma ka amsar ne daga Furfesan fannin yanayi, Abubakar Sadik Umar, na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawan Najeriya.
To sai a kasance da mu makon gobe don jin kashi na biyu kuma na karshe na wannan tambayar da kuma wasu tambayoyin. Yanzu a madadin Farfesan yanayi a Jami’ar Modibbo Adama, Abubakar Sadik Umar, da wakilinmu a Adamawa, Mohamed Salisu Garba, ni Ibrahim Ka-Almasih Garba ke cewa sai makon goben idan Allah ya kai mu. Wassalam.
Ga cikakken sautin shirin: