Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU *Yaya man jirgin sama ya ke? Yaya ake hako shi? Yaya jirgin sama ke shan man? *(Shugabannin Kasa Matasa 2)


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.

Tambaya 1:

"Assalamu Alaikum, Muryar Amurka. So na ke a yi min karin haske kan man da jirgin sama ya ke amfani da shi. Wai shin mene ne bambancin shi da man fetur ko iskar gas? Ko yaya ake hako man jirgin?”

Mai tambaya: Ado Turaki Askira, jahar Bornon Najeriya.

Tambaya 2

Sai kuma kashi na biyu na amsar tambayar nan mai cewa:

(1)Wai Don Allah a wadanne kasashe ne matasa suka Samu damar kama madafan mulki?

(2)kuma ko matasan sun taka rawar gani a zamanin mulkin nasu?”

Idan an tuna, Mai tambayar, shi ne: Dalhatu manjos Gobir, Samaru Busstop Zaria, Jahar Kaduna, Najeriya.

Amsar Tambayoyin

To bari mu fara da amsar tambaya kan man jirgin sama. Idan Ado Turaki Askira na tare da mu, ga amsar da wakilin Muryar Amurka a Minna, Mustapha Nasiru Batsari, ya samo ma ka daga Shugaban Kungiyar Dillalan mai na Depo din Minna, Jahar Nejan Najeriya, Alh. Adamu Ahmad Erana.

Hakazalika, Idan Malam Dalhatu Manjos Gobir na tare da mu, ga kashi na biyu na amsarka game da matasan shugabannin duniya, da wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isa Lawan Ikara, ya samo daga Mataimakin Furfesan Tarihi, wanda zai dora daga inda ya yi ta zayyana kasashen da aka samu shugabanni matasa.

To sai a kasance da mu makon gobe don jin kashi na uku na amsoshin tambaya kan shugabancin matasa a kasashen duniya da kuma amsoshin wasu tambayoyin. Yanzu a madadin wadanda su ka amsa ma na tambayoyin: Alhaji Adamu Ahmad Erana, da Mataimakin Furfesa, Salisu Bala, da wakilan Muryar Amurka: Isa Lawan Ikara da Mustapha Nasiru Batsari, da wadda ta hada ma na sautin, Julie Leathers Gresham, da Injiniyanmu, ni Ibrahim Ka-Almasih Garba ke cewa sai makon goben idan Allah ya kai mu. A yi saurare lafiya:

07-02-22 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:12 0:00

XS
SM
MD
LG