Tsohon jakadan kasar Birtaniya a Amurka, ya yi ammar cewa, janyewar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi daga matsayar da aka cimma kan nukiliyar Iran, “babbar barnace ta fuskar diplomasiyya” da shugaban ya yi ga abin da tsohon shugaban Amurka Barack Amurka ya bari a baya, a cewar wasu sabbin bayanai da aka kwarmata, wadanda wata jaridar kasar ta Birtaniya ta wallafa.
Jaridar The Mail ce ta wallafa sabbin bayanan a yau Lahadi, wadanda tsohon jakada Kim Darroch ya aika.
A makon da ya gabata, jaridar ta wallafa wasu bayanan da aka kwarmata, wadanda suka nuna Darroch yana muzanta Shugaba Trump da gwamnatinsa.
A ranar Larabar da ta gabata kuma, Darroch ya sauka daga mukaminsa bayan bullar bayanan na sirri a baina jama’a, lamarin da ya sa Shugaba Trump ya shiga shafinsa na Twitter ya kira Darroch a matsayin “shasha mai ji-ji da kai”, ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta kara hulda da shi ba.
Su dai wadannan bayanai da aka wallafa a jaridar, sakonni ne na waya da manyan jami’an kasar Birtaniya ne kadai ya kamata su karanta.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 22, 2021
An Sallami Shugaban Hukumar Dake Kula Da Muryar Amurka
-
Janairu 21, 2021
Jam'iyyar Democrat Ta Karbe Iko a Dukkan Majalisun Amurka
-
Janairu 21, 2021
Amurka Ta Sake Bude Kofa Ga Baki Daga Ko'ina a Duniya
-
Janairu 21, 2021
An Rantsar da Joe Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46