Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Canada Suna Jagorancin Taron Kasashe 20 Kan Koriya A Vancouver


Amurka da Canada suna daukar dawaniyar wani taro yau Talata a birnin Vancouver wanda zai maida hankali kan matsawa Koriya ta Arewa lambar ta yi watsi da shirye shiryen ta na Nukiliya.

Amurka da Canada suna daukar dawaniyar wani taro yau Talata a birnin Vancouver wanda zai maida da hankali kan matsawa Korea ta Arewa lambar ta yi watsi shirye shiryen ta na Nukiliya da take yi.

Sakateren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson da takwaran aikinsa na Canada Chrystia Freeland za su kawo jami’ai 20 daga kasahe dabam dabam domin tattaunawa akan hanyoyin da suka fi dacewa na kaddamar da takunkumi domin hana Koriya ta Arewa kaucewa matakan da MDD ta tsara akan wannan batu.

Darektan shirya manufofi a ma’aikatar harkokin wajen Amurka Brian Hook y ace kafin ganawar, shugabanni suna son su nuna cewa akwai hanya ta diflomasiyya da za’a iya amfani da ita domin mafita, bayan da wani jami’i yace ba za ‘a tattauna akan mafita ta hanyar soja ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG