Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Sun Cimma Matsaya Akan Cinikayya Tsakaninsu


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban China Xi Jinging

Bayan sun yi barzanar kara haraji akan kayayyakinda suke sayarwa juna shugabannin Amurka da na China sun amince su dakatar da duk wani karin haraji tare da zaunawa su zana jadawalin kasuwanci tsakaninsu

Amurka da China sun cimma matsaya na daina sawa juna haraji mai yawan gaske akan kayayyakin da suke cinikayya a tsakanin su.

Wannan yana zuwa kwana daya bayan da aka cimma yarjejeniyar data tanadi kasar ta China ta kara dayen kayayyaki a Amurka akan farashi mai rahusa domin rage gibin cinikayya da China.

Sakataren Baitulmalin Amurka Steven Mnuchin ya fada wa gidan talabijin na Fox cewa kasashen biyu masu karfin arziki sun samu ci gaba sosai a tattaunawar su.

Yace yanzu haka sun amince akan jadawalin daidaitawa akan batutuwa da suka tsara.

Kanfanin dillacin labarai na China Xinhua ya ambato mataimakin Prime minister Liu He wanda shine ya jagoranci tawagar ta China a tattaunawar da suka yi da Amurka a satin da ya gabata yana cewa ba shakka kasashen biyu sun cimma matsaya akan ba zasu sake tada jijiyar wuya ba game da harkokin kasuwanci, kuma zasu dakatar das batun haraji tsakanin su a halin yanzu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG