Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Za Su Ci gaba Da Tattaunawa Kan Cinikayya


Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce a mako mai zuwa wasu manyan jami’an Amurka za su je kasar China, domin ci gaba da tattaunawa don samar da masalaha tsakanin kasashen biyu a fannin cinikayya.

Sanarwar da aka fitar jiya Talata, ta ce sakataren ma’aikatar kudi Steven Mnuchin da jami’in cinikayya Robert Lighizer za su gana da mataimakin Firimiya Liu He a birnin Beijing ranar 30 ga watan nan na Afrilu.

Bangarorin biyu dai za su tattauna kan batutuwan da suka hada da fasahar da juna ke da su da tilasta musayar fasaha da kuma kudaden haraji da ba a karba da kuma kayayyakin amfanin gona.

Fadar White House ta ce mataimakin Firimiya Liu shine zai jagoranci tawagar jami’an China zuwa Washinton a makon gaba domin ci gaba da tattaunawar ranar 8 ga watan Mayu.

Amurka da China sun sha yin tattaunawa tun farkon shekarar nan domin sasantawa kan rikicin cinikayya da ya fara tun shekarar da ta gabata, lokacin da shugaban kasa Donald Trump ya saka harajin Dala biliyan 250 akan wasu kaya da China ke shigarwa Amurka. Haka kuma ita kanta China ta mayar da martani ta hanyar ‘kara haraji akan kayan Amurka har na Dala biliyan 110.

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG