Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun yi na'am da shirin kafa gwamnatin hadin kai a Libya


Sakataren harkokin wajen Amurka akan shirin kafa gwamnatin hadin kai a kasar ta Libya

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice dukan sun yi maraba da kokarin da majilisar dokokin kasar Libya tayi na samar da gwamnatin hadin kan kasa.

To sai dai kuma sun bayyana damuwar su akan yadda wasu ‘yan majilisar suke yiwa wannan shirin barazana musammam wadanda basa goyon bayan tsarin.

Rahotanni sun bayyana cewa da yawan ‘yan majilisar da suka kai har 100 daga cikin 196, wadanda ke Tabruk kuma sune duniya ta amince da su, sune suka ce sun amince da wannan tsarin, wanda zai kawo su cikin gwamnati guda da bangaren gwamnatin kasar dake da hedikwata a Tripoli.

Suka ce amma kuma ba wai sun amince da wannan tsarin bane domin ana musu wata barazana.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada jiya Laraba cewa Amurka na goyon bayan wadannan ‘yan Libyan da suke kokarin ganin an samar da wannan gwamnati ta hadin kan kasa.

A lokacin da Kerry ke bayani a gaban ‘yan majilisar dokokin Amurka game da bukatar dake akwai na ganin an samar da maslaha akan rikicin siyasar kasar Libya, wanda ya jefa kasar cikin halin rudu da damuwa tun lokacin mutuwar tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG