Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Samaliya Sun Kai Sumame Kan Kungiyar Al'shabab


Alshabab

A yau talata sojojin Amurka da na Somaliya sun kai wani samamen hadin gwiwa akan sansanin ‘yan kungiyar al’shabab, inda suka hallaka da kuma kama ‘ya’yan kungiyar da dama.

Wani jami’in tsaron kasar ta Somalia Mohammed Nur Gabow ya fada wa Sashen Somliyanci na voa cewar sojojin Amurka ne suka dauki jagorancin samamen wanda ya auna jami’an kungiyar ta al-Shabab.

Mazauna kauyen Toratorow mai tazarar kilomita 100 kudu maso yammacin birnin Mogadishu sun ce sojojin sun sauko ne daga wani jirgi mai saukar angulu a kusa da kauyen daga nan suka doshi inda suka kai samamen a kasa.

Gabow ya ce an kwashe sa’oi biyu ana gudanarda samamen kuma sojojin basu sami fuskanci wata jayyaya ba, amma bai bayyana wadanda aka kai samamen akan su ba ko kuma adadin mutanen da aka kama da kuma wadanda aka kashe.

XS
SM
MD
LG