Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Hukumar Tsaron Cikin Gidan Tace Ta Iya Tantance 'Yan Gudun Hijiran Syria


'Wasu 'yan gudun hijira daga kasar Syria

Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka tana kare kanta cewa zata iya tantance 'yan gudun hijira daga Syria wadanda suka nemi mafaka a Amurka, bayan mummunar harin ta'addancin da aka kai a Paris, har jami'an ma'aikatar suna cewa gwamnoni wasu jihohi wadanda suke son suki karbar 'yan gudun hijirar kan dalilan tsaro da cewa, fargabar da suke da ita bata da tushe.

Da yake magana da manema labarai ta wayar tarho jiya Litinin, mukaddashin sakataren ma'aikatar Alejandro Mayorkas, yace yana da kwarin guiwa zasu tabbatarwa gwamnonin cewa babu wani dalili na fargaba.

Gwamnonin wasu jihohi fiyeda 24 ne suka ayyana turjiya na karbar 'yan gudun hijira daga Syria a jihohin nasu, bayan da aka gano cewa daya daga cikin mutanen da suka kai hari a Paris, dan ta'adda ne da ya saci-jiki yabi 'yan gudun hijira da suke gudu daga yakin basasar kasar Syria ya shiga Turai.

Gwamnonin sun nemi da a kawo karshen shirin sake tsugunarda 'yan gudun hijira kimanin dubu 10 daga Syria anan Amurka badi,a muhawara da ake yi anan Amurka, shigen wadanda ake yi a kasashen Turai cewa karbar ‘yan gudun hijiran yana jefa tsaron kasashen cikin hadari.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG