Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kudurin Yiwa Dokar Shige da Fice Garambawul


Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Paul Ryan

A kuri'un da suka kada akan kudurin yiwa dokar shige da fice garambawul da shugaba Trump ya marawa baya, 'yan majalisar wakilan kasar da gagarumar rinjaye suka yi watsi da kudurin

Majalisar Wakilai ta Amurka, ta yi watsi da gagarumin rinjaye da wata bukata wacce ta nemi da a yi wa tsarin shige da ficen kasar garanbawul, inda suka nuna halin ko-in-kula da magiyar da shugaba Donald Trump ya yi kan su amince da kudurin dokar.

Kuri’ar da aka kada a jiya Laraba, ta nuna cewa wadanda suka ki amincewa da kudirin sun samu kuri’u 301 yayin da wadanda suka zabi akasin hakan suka samu kuri’u 121, inda a bangaren ‘yan Democrat aka samu kwakkwaran hadin kai na adawa da kudurin, yayin da aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Republican.

Shugabannin ‘yan Republican sun amince da shi wannan kuduri, to amma da yawa daga cikin ‘yan gani-kashenin-jam’iyyar ta Republican, sun ki amincewa da kudurin, domin a cewarsu, hakan zai bai wa daruruwan dubban matasan bakin haure da ke zaune a nan Amurka, damar samun takardun iznin zama ‘yan kasa, wadanda a shekarun baya iyayensu suka shigo da su ba bisa ka’ida ba, lamarin da ‘yan adawan suka ce tamkar “afuwa” ne ga wadanda suka karya doka.

Wannan kaye` da kudurin ya sha, sharar fage ne ga aniyar shugaba Trump ta samar da wata kofa da za a fara aiwatar da dokar hana raba ‘ya’ya da iyayensu idan hukumomi suka kama su, a lokacin da suke kan tsallaka kan iyakar Mexico zuwa cikin Amurka ba bisa ka’ida ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG