Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na aiki da Najeriya kan yakar cin hanci da rashawa -John Kerry


Shugaban Najeriya Buhari da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry

Akwai yiwuwar sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya dan fuskanci matsin lamba a taron yaki da cin hancin da Firaministan Birtaniya David Cameron ke karbar bakuncin taron a birnin London.

Firaminista Cameron ya fada tun kafin ranar taron cewa, hakika cin hanci da rashawa makiyan samar da ci gaba ne, hakan ne yasa kasashe masu arziki irinsu Birtaniya da Amurka su amsawa duniya neman mafita.

Manufar taron shine, amincewa da duk dabarun fallasawa da kuma hukunta masu aikata wannan laifin a duniya. Taron zai hada da shugabannin Afghanistan, Colombia da kuma Najeriya.

A wani jawabi ga ‘yan jami’ar Oxford, Mista Kerry ya fadawa dalibai cewa, Amurka na nan tana aiki da Najeriya don yakar cin hanci da rashawa ba ji ba gani. Najeriya dai tana ji tana gani an fitar da Biliyoyin Daloli daga kasar cikin almundahana.

Kama daga kudaden bangaren harkar makarantu, harkar lafiya, ayyukan gwamnati da na sababbin ayyuka, aka fitar tare da boyewa a bankuna daban-daban dake kasashen duniya. Kerry yace ba ga kasashen masu tasowa kadai ba, har da masu arziki za a sawa idanu.

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG