Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Iya Zama Kasar Da Coronavirus Ta Fi Addaba - WHO


Daraktan Hukumar Lafiya Ta Duniya

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ta ce Amurka na iya zama kasar da cutar Coronavirus ta fi addaba nan ba da dadewa ba.

Mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniyar, Margaret Harris, ta fadi a wani taron manema labarai a Geneva cewa, wannan hasashe na hukumar, ya biyo bayan dada yawa da sabbin kamuwa da cutar ke yi a Amurkar.

“Yanzu mu na ganin dimbin sabbin kamuwa da cutar a Amurka, saboda haka, Amurka na fuskantar yiwuwar samun kanta cikin wannan yanayi,” a cewar Margaret.

Ta kara da cewa, “a halin yanzu, ba za mu iya cewa ko hakan zai faru ba, to amma akwai yiwuwar faruwar hakan.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG