Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Karfafa Yarjeniyoyin Tsaro, Tattalin Arziki Da India


Fraministan India Modi da mai masaukinsa shugaban Amurka Donald Trump

A lokacin da ya kawo ziyara nan Amurka Fira ministan India Nerendra Modi ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a Fadar White House inda suka yi alkawarin karfafa dangantakar yarjeniyoyi tsakaninsu kamar Amurka da kawayenta na kud-da-kud.

Shugaban Amurka Donald Trump da Fira ministan India Narendra Modi sun yi alkawarin aiki tare wajen karfafa yarjajjeniyoyin tsaro da na tattalin arziki dake tsakaninsu.

Kasashen biyu na hankoron hada kai wajen abin da ya shafi na'urorin tsaro masu inganci irin yadda Amurka kan yi da kawayenta na kud-da-kud, a cewar wani bayanin Fadar White House da aka fitar da yammacin jiya Litini.

Firaministan na India, wanda ya bayyana tattaunawarsa da Shugaba Trump da cewa ta yi tasiri, ya baiwa Trump wata kyauta ta karramawa a wurin shakatawa na Rose Garden bayan kammala tattaunawar ta su.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG