Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Zargin Syria Da Kai Harin Makami Mai Guba


Ga dukkan alamu, za a sake sa kafar wando guda tsakanin Amurka da kasar Siriya saboda zargin da ake ma Siriyar da sake amfani da makaman guba.

Amurka ta ce akwai alamun da ke nuna cewar, gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya na amfani da makamai masu guba kuma ta gargadi Siriyawa su dakatar da shi.

A jiya Talata ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, ta yi imanin cewar, sojojin Siriya na da hannu a wani harin da ake zargin na iska mai guba ne mai suna Chlorine Gas da aka kai ranar Lahadin da ta gabata, a arewa maso yammacin Siriya.

Mai magana da yawun Amurka ta ce, jami'ai suna ci gaba da tattara bayanai game da harin da ake zargin Syria da kaiwa, amma ta ce "idan gwamnatin Assad ta yi amfani da makamai masu guba, Amurka da abokanta za su dauki mataki cikin sauri da kuma dacewa."

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG