Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bar Wasu Sojojinta Su Tsare Filayen Hakar Man Syria


Sakataren tsaron Amurka Mark Esper, ya ce za su bar wasu dakarun Amurka da za su tsare filayen hakan mai da ke arewa maso gabashin Siriya, domin kada su fada hannunn mayakan ISIS.

Wani ayari mai motoci sama da 100 cike da dakarun Amurka ya ketara zuwa Iraki daga Siriya a jiya Litinin, a wani bangare na umurnin da Shugaba Donald Trump ya bayar na janyewar dakarun Amurka daga arewacin Siriya.

Amma Esper ya ce, har yanzu wasu sojojin Amurkan suna ci gaba da sintiri a kusa da filayen hakar man tare da mayakan Kurdawan da ke jagorantar gamayyar dakarun SDF.

A ranar Lahadin da ta gabata, Shugaba Trump ya wallafa a shafin Twitter cewa, “filayen man na karkashin ikonsu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG