Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bukaci Turkiya Da Isra'ila Su Daidaita Da Juna


Sakataren Ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry da Firai Ministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan,
Sakataren Ma'aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry da Firai Ministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan,
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi kira ga Turkiya da kuma Isra’ila su hamzarta sake kulla huldar diplomasiya tsakaninsu, yace kasashen suna da muhimmiyar rawar da zasu taka a warware matsalolin Gabas Ta Tsakiya.

Kerry yana Istanbul yau Lahadi inda zai gana da Firai Ministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu da Firai Minista Recep Tayyip Erdogan.

A wani taron manema labarai na hadin guiwa da ministan harkokin kasashen ketaren, Kerry ya bayyana cewa, yana da muhimmanci Turkiya da Isra’ila su cimma matsaya dangane da diyyar da za a biya a kan abinda ya kawo rashin jituwa tsakanin kasashen shekaru uku da suka shige, lokacin da ‘yan kasar Turkiya takwas da kuma wani Ba’amurke dan asalin kasar Turkiya suka mutu a wani sumame da Isra’ila ta kai kan ayarin kananan jiragen ruwan Turkiya dake kan hanyarsu zuwa zirin Gaza.

Turkiya da Isra’ila dukansu muhimman abokan kawancen Amurka ne, muna kuma kyautata zaton amincewa da sake daidaita dangantaka tsakanin kasashen zai taimaka wajen bude kofar hulda mai girma.
Dangane kuma da rikicin da ake yi a makwabciya Siriya, Kerry yace, Amurka da Turkiya suna da manufa daya na ganin an mika mulki cikin kwanciyar hankali a Siriya. Yace Turkiya tayi kokari ainun wajen tallafawa ‘yan gudun hijirar kasar Siriya dake cikin kasarta.
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG