Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dage Dokar Shiga Jirgin Sama Da komfutar Hannu


Dalibai a kasar Indiya su na nuna sabuwar kwamfutar mai suna "Aakash" wato "Samaniya" kenan da yaren Hindi
Dalibai a kasar Indiya su na nuna sabuwar kwamfutar mai suna "Aakash" wato "Samaniya" kenan da yaren Hindi

A jiya lahadi ne Amurka ta dage dokar hana shiga cikin jirigin sama da komputar hanu daga Abu Dhabi, helkwatar hadaddiyar daular kasashen larabawa

Bayan da kamfanin jiragen fasinjar kasar Etihad ya aiwatar da sabbin matakan tsaro.
Dokar ta fara aiki ne cikin watan Maris wacce ta shafi jirage da suke zuwa Amurka kai tsaye daga tashar jiragen sama 10 a yankin Gabas ta tsakiya, saboda damuwar da jami'an Amurka suke da ita cewa akwai yiyuwar 'yan ta'adda su boye bama bamai cikin na'urorin masu kwa-kwalwa.
Kamfanin Etihad wanda yake jigila 45 ko wani mako daga Abu Dhabi zuwa Amurka, yayi marhabin da wannan mataki.
Wani kakakin ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ya yabawa kamfanin jiragen saman saboda sabbin matakai da ya dauka, wadanda ba'a bayyana su ba, ya kara da cewa "matakin zai kasance abun koyi ga jirage da suke zirga-zirga cikin gida da kuma ketare."
Har yanzu dokar tana ci gaba da aiki kan jiragen sama da suke tashi kai tsaye zuwa Amurka daga tashoshin jirgin-sama a Kuwait, da Jordan, da Masar, da Turkiyya, da Saudiyya, da Morocco, da Qatar, da kuma Dubai

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG