Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fara Shirin Gina Ganuwa Tsakaninta Da Mexico


Wani yankin kan iyakar Amurka da Mexico
Wani yankin kan iyakar Amurka da Mexico

Gwamnatin Amurka ta fara shirye-shiryen fara ba da aikin kwangilar gina ganuwa akan iyakar Amurka da Mexico domin cika daya daga cikin manyan alkawuran da shugaba  Donald Trump ya yi a lokacin kamfe.

Jami’an kare iyaka da fasa-kori na Amurka za su fara karbar takardun tsarin aikin ginin katangar a mako mai zuwa.

Daga nan kuma Ma’aikatar za ta bukaci maginan da su ba da adadin kudin da za’a kashe, bayan an duba daga nan kuma sai a fara ba da kwangilar a tsakiyar watan Afrilu.

Wannan kusan shi ne tsarin shirin gini mafi sauri da gwamnati ke kokarin aiwatarwa.

Sai dai ma’aikatar kula da iyaka da fasa-kori ta kwastam, wani bangare na ma’aikatar tsaron cikin gida ba ta ba da takamaiman inda za’a fara ginin katangar ba.

Shugaban kasa Trump ya fadawa mahalarta taron masu tsatstsauran ra’ayi a jiya juma’a cewar, shirin ginin katangar a shirye ake da aiwatar da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG