Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fitar Da Sabbin Ka'idojin Ba Da "Visa"


Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo

Hukumomin kasar ta Amurka dai sun ce, wannan sabon tsari zai shafi kusan ‘yan kasashe waje miliyan 15, amma  ba zai hada da jami’an diplomasiyya ba

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta fito da wani sabon tsarin ba da takardar visa, inda za ta rika neman masu niyyar zuwa kasar su bayar da adreshin kafafen sada zumuntarsu.

Hukumomi za su bukaci bayanai kan adreshin Facebook, Instagram, WhatsApp da na kafar aika sakonnin na email da kuma bayanai na wayoyin salula.

Wadannan sabbin ka’idoji da Amurkan ta fitar ga masu neman yin kaura zuwa kasar da masu ziyara, na bukatar mutum ya ba da sunan da yake amfani da shi a kafafen sada zumunta da adreshin email da kuma lambobin wayoyinsa da ya yi amfani da su cikin shekaru biyar da suka gabata.

Hukumomin kasar ta Amurka dai sun ce, wannan sabon tsari zai shafi kusan ‘yan kasashe waje miliyan 15, amma ba zai hada da jami’an diplomasiyya ba.

Sannan za kuma a tambayi masu neman visar, ko wani na su na jika ya taba mu’amulla da ‘yan ta’adda.

Tun dai a watan Maris din bara, aka mika bukatar fara amfani da wannan tsari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG