Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta ja kunnuwan amurkawa mazauna Afghanistan


John Kerry, sakataren harkokin wajen Amurka

Biyo bayan yadda kungiyar Taliban suka kara kamari wajen kai hare hare a kasar Afghanistan gwamnatin Amurka ta ja kunnuwan 'ya'yanta dake zaune kasar

Amurka ta ja kunnen Amurkawan dake zaune a kasar Afgahnistan da su kwana cikin shiri saboda mayakan ‘yantawayen kasar na shirin kai hare-haren a kan gidajen baki inda ake sauke mutanen kasashen waje dake birnin Kabul a cikin watan nan.

Sai dai sanarwar tace ba tabbass na ainihin lokaci ko takamammun wuraren da za’a kaiwa farmakin ko ma ainihin fasalin farmakin kansa.

A ‘yan wattanin nan mayakan Taliban sun sha anfani da ‘yan kunar bakin wake wajen kai hare-hare akan mutanen Afghanistan da ‘yan kasashen ketare, ciki harda irin wadanan gidajen na sauke baki.

XS
SM
MD
LG