Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kaddamar Da Tauraron Binciken Sararin Samaniya Artemis 1


Ofishin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka
Ofishin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

Da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Nuwamba ne aka harba wani tauraron binciken sararin samaniya mai suna Artemis 1 daga cibiyar binciken sararin samaniya ta Kennedy, inda ya yi tafiya zuwa duniyar wata, wani babban mataki na sake tura dan Adam zuwa duniyar wata nan da shekarar 2025.

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka ta sanya sunan shirinta zuwa sararin samaniya, Artemis, sunan shirin aikin sama jannati Apollo, da ya yi nasarar sauka a wata a zamanin Apollo. Apollo ya yi tafiyarsa ta karshe zuwa duniyar wata a watan Disamba na 1972.

"Dukkanmu mun shiga tarihin ganin wani abu na musamman farkon kaddamar da Artemis, matakin farko na dawo da kasarmu zuwa duniyar wata da duniyar Mars," Kamar yadda Daraktan ƙaddamar da Artemis 1 Charlie Blackwell-Thompson ya gaya wa ƙungiyar ƙaddamarwa bayan an tashi zuwa sama. "Abin da kuka aikata zai zaburar da al'umma masu zuwa."

An shafe sama da shekaru goma ana aiki kafin Ƙaddamarwar Artemis 1, kuma ya fuskanci jinkiri akai-akai saboda yanayi da matsalar fasaha. Kumbon Orion zai yi tafiyar kimanin nisan mil 40,000 nesa da wata, nesa da kowane kumbon da dan Adam ya auna, a cewar NASA. An shirya za a karasa gwajin jirgin Artemis 1 tare da tsundumar Orion a Tekun Pacific a ranar 11 ga Disamba.

"Nasarar ƙaddamar da Artemis 1 ya biyo bayan ƙoƙarin haɗin gwiwa don gano sararin samaniya, da samun ci gaba mai dorewa a duniyar wata daga baya cikin shekaru goma, da kuma shirya gudanar da aikin ɗan adam mai tarihi zuwa duniyar Mars," in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a cikin wata sanarwa.

"Ta shirin Artemis, Amurka tana kulla haɗin gwiwar binciken sararin samaniya da ya fi hada kan kasashe da dama na duniya a tarihi, wanda ke mai da hankali kan yin binciken kimiyya da fasaha don haɓaka ƙoƙarinmu na sararin samaniya. Mayar da fa'idodi da yawa ga duniyarmu ta gida, ”in ji Sakatare Blinken. "Muna sa ran ci gaba da aiki tare da abokan hulɗa na duniya kan ayyuka na gaba."

Da Yarjejeniyar Artemis, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amukar da NASA suna tattaro al'ummomi ta hanyar tsarin ka'idoji da aka kafa a cikin yarjejeniyar sararin samaniya ta 1967 don jagorantar binciken sararin samaniya, da kuma kafa mataki don haɗin kai na lumana, da daukar nauyi, da haɗin kai a sararin samaniya.

Tare da samun nasarar ƙaddamar da Artemis 1, Hukumar NASA na kusa da mayar da ɗan adam zuwa duniyar wata. A matsayin ɗan sama jannati na ƙarshe da ya yi tafiya a sararin samaniyar wata, Eugene Cernan, ya ce "mun tashi kamar yadda muka zo kuma, in Allah ya yarda, za mu dawo, tare da salama da bege ga dukan 'yan adam."

XS
SM
MD
LG