Accessibility links

Amurka Ta Soki Shirin Isra'ila Na GIna Sabbin Gidaje A Yankunan Falasdinu.


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da PM Isra'ila Benjamin Netanyahu, a birnin kudus, ranar 20 ga watan jiya.

Amurka ta ta soki sanarwar da Isra’ila t bayar na shirin gina gidaje dubu uku ga ‘yan kaka-gida a yammacin kogin Jordan da kuma a gabshin birnin kudus, bayan nasarar da hukumomi yankin Falasdinu suka samu na amincewar Majalisar Dinkin Duniya.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton, ta fada jiya jumma’a cewa gwamnatin Obama kamar sauran gwamnatocin Amurka da suka wuce, sun bayyana cewa irin wadannan matakai suna maida hanun agogo baya a yunkurin shawarwarin wanzarda zaman lafiya.

Clinton tayi magana ne a wani taro da wata cibiya mai tsara manufofi kan gabas ta tsakiya ta shirya, inda minisocin harkokin wajen Isra’ila da na tsaron kasar Avigdor Lieberman da Ehud Barak suka halarta.

Jami’an Isra’ila wadanda suka zanta da kafofin yada labarai bisa sharadin ba za a bayyana sunayensu ba, sun ce gwamnatin PM Benjamin Netanyahu ta bada umurnin a aiwatar da gine ginen, da kuma aikin farko farko na kebe wasu sassa a yammacin na kogin Jordan din.
XS
SM
MD
LG