Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tabbatar Da Mutuwar Sojanta Na Hudu A Nijar Sakamkon Harin Kwanton Bauna.


Taswirar jamhuriyar Nijar, yake nuna inda aka kaiwa sojojin hari.
Taswirar jamhuriyar Nijar, yake nuna inda aka kaiwa sojojin hari.

Ranar Laraba aka kaiwa sojojin hari kan iyakar Nijar da Mali yayinda suke sintiri na hadin guiwa.

Rundunar sojojin Amurka ta bayyana cewa an kashe sojanta na hudu a wani harin da 'yan kungiyar ISIS suka kai kan dakarun a jamhuriyar Nijar. Jiya jumma'a ce rundunar ta bada wannan karin bayani.

Jami'an mayakan Amurkan sun ce sojan ya bace ne bayan wani mummunar kwanton bauna da mayakan suka kai musu yayinda suke sintiri na hadin guiwa tareda sojojin Nijar ranar Laraba kusa da kan iyakar kasar da Mali. Rundunar tace a jiya jumma ne dakarun Nijar suka gano gawar sojan na hudu bayan da suka gudanar bincike mai tsanani.

Tuni rundunar ta tabbatar da mutuwar sojojinta uku bayan harin. Wani jami'in tsaron Amurka ya gayawa MA ranar Alhgamis cewa sojojin daga rundunar nan ce da ake kira Green Berets da turanci.

Haka nan an kashe sojojin Nijar su hudu a yayin da aka kai harin. An raunata sojojin Nijar 8 da na Amurka biyu.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin,amma jami'an Amurka sun ce suna zargin reshen kungiyar ISIS dake kasar. Kakakin rundunar sojojin Amurka dake kula da shiyyar Afirka tace zasu farauto wadanda suke da hanu akai harin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG