Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Taba Nijar Gudummuwar Kayan Aikin Soja


Shugaban kasar Najeriya Buhari da shugaban kasar Nijer Issoufou a Niamey, Yuni 3, 2015.

Amurka ta taimakawa sojojin janhuriyar Nijer da kayayakin aiki wadanda sojojin zasu amfani da su wajen samun bayanan da suka shafi tsaro,

Kayayyakin da Amurka ta ba Jamhuriyar Nihar taimako sun hada da da jiragen samun bayanai da jiragen hango abokin gaba guda biyu.da kuma motocin sojoji guda talatin da uku.

Idi Barau jami’in dake kula da harkokin sadarwa a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Nyamie yace kudin motocin kadai ya kai saifa biliyan bakwai, jiragen da kayan aikin da suke dauke da su kamar kamarori, da na’urorin dake basu damar hango abokan gaba, sun kai kudi saifa biliyan goma sha uku.

A nasa bangaren ministan Muhammadu ya yaba matuka da taimakon na Amurka, yace kasar Amurka ta nuna a zahiri niyyarta ta taimakawa Jamhuriyar Nijar, a karshen jagorancin shugaban kasar Yusuf Muhammadu da kayayyakin aiki na sojoji, domin kara basu damar tabbatar da tsaron iyakokinmu da al’umma da kuma kaddarori

Za a kai kayan na sojoji ne a yankin Durku, wadanda sojojin zasu yi amfani da su, wajen samun bayan da suka shafi tsaro.

Daga Nyamai, ga Rahoton wakilin Sashen Hausa Yusuf Abdullahi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG