Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tace Pakistan Zata Kai Hari Kan Kungiyoyin Taliban da na Haqqani


Amurka tace kasar Pakistan ta kuduri wani sabon yunkurin kai hari akan kungiyoyin Taliban da na Haqqani a wuraren jinsunan dake kan iyaka da Afghan.
Manyan jami’an Amurka na Ma’aikatar Harkokin Waje suka bayyana manufofin ranar Litinin da dare a Birnin Islamabad.
Tun can farko Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da wasu jami’an diflomasiyar Amurka sun ci abincin dare da Firayim Ministan Pakistan Nawaz Sharif da wasu mukarrabansa.
Jami’an Amurka dake cikin tawagar Kerry sun shaidawa manema labarai cewa jami’an Pakistan sun sha alwashin kai hare-hare akan sansanonin ‘yan Taliban dake Arewacin Waziristan.
A wannan karon Pakistan ba zata damu da ko wasu Taliban nakwarai ne ba ko mugayen ne. Zata daukesu duk abu daya. Haka kuma a karon farko Pakistan ta nuna aniyarta na yakar kungiyar Haqqani da take da tushe a Afghanistan amma kuma tana samun goyon bayan wasu jami’an tsaron Pakistan din.
Wani babban jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka yace Amurka na shirin aikawa Pakistan dala miliyan 250 a matsayin wani sabon taimako domin ta sabunta gine-gine a Arewacin Waziristan da wuraren da jinsunan kasar dake karkashinta suka mallaka. Kudin zai kuma taimaka wurin sake tsugunar da wadanda aka rabasu da muhallansu alatilas a kasar.

XS
SM
MD
LG