Accessibility links

Amurka Tana Daf Da Fadawa Kunci, Idan Ba'a Cimma Yarjejeniya kan.....

  • Aliyu Imam

Zauren majalisar dokokin Amurka
Yau litinin, ‘yan majalisar dokokin Amurka zasu sake hallara domin yunkurin karshe na kuacewa dokar da zata ayyana Karin kudin haraji da ragin kudaden da Gwamnati ke kashewa domin gudanar da ayyukan yau da kullun.Dokar da zata fara aiki daga gobe daya ga watan Janaiaru na sabuwar shekara.
Tilas ne duk wata yarjejeniyar da aka cimma da farko ta ratsa ta hanun majalisar dattijai, wacce zata koma zama kamin tsakar ranar litinin din nan, bayan da aka kwashe wunin jiya lahadi ana gudanar da shawarwari masu zurfi, da a karshe basu cimma kome ba.

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, yayi wata ganawa a kebe tare da jagoran maras rinjaye a majalisar dattawan Amurka Mitch McConnel,a daidai lokacin da hadin gwiwar wakilan jam’iyyun Democrat da na Republican ke kokarin samun daidaituwa domin rage bambance-bambancen dake tsakaninsu game da karin kudin haraji kan masu hanu da shuni, da kuma zabtarewar da za ayiwa kudadenda gwamnati take kashewa.

Amma anji shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka Harry Reid yana cewa gibin da yake tsakanin sassan biyu suna da “muhimmanci kwarai”, yayinda shugaban maras rinjaye Mitch McConnell, yake cewa dan abunda ya rage yana buktar "karfin hali ko kuma kwarin guiwa” tsakanin wakilan majalisun, domin a cimma daidaito.

Idan har majalisar dattawan wacce ‘yan Democrat suke da rinjaye ta amince da yarjejeniyar, to tilas majalisar wakilai da ‘yan Republican suke da rinjaye ita ma ta kada kuri’ar amincewa da daftarin. Sannan daga bisani, shugaban kasa ya rattabawa kudurin hanu a maraicen litinin din nan, wanda hakan zai kaucewa dokar da zata kara haraji kusan kan duk wani dan kasar Amurka daga Talata, 1 ga watan Janairu 2013.
XS
SM
MD
LG