Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tasa Ido Sosai Kan Zaben Najeriya, inji Ma'aikatar harkokin Wajen Amurka


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.

Bisa ga dukkan alamu, bada wasa Amurka take daukar wannan zaben da ake a Nigeria ba, saboda muhimmancin Nigeria din a wurin Amurka. A matsayin Nigeria kasar da tafi kowace kasar Afrika yawan mutane, karfin tattalinta na arziki, zamanta daya daga cikin kasashen da Amurka ke samun aksarin man fetur dinta.

Bisa ga dukkan alamu, bada wasa Amurka take daukar wannan zaben da ake a Nigeria ba, saboda muhimmancin Nigeria din a wurin Amurka.

A matsayin Nigeria kasar da tafi kowace kasar Afrika yawan mutane, karfin tattalinta na arziki, zamanta daya daga cikin kasashen da Amurka ke samun aksarin man fetur dinta daga wurinta da kuma irin rawar da Nigeria din ke takawa a harkokin da suka shafi kasashen Afrika da na duniya baki daya, yasa Amurka take maida hankali sosai ga wannan zaben – da kuma masu gudanar da shi, kamar yadda mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Afrika:

“Mun kyalla ido da kyau muna kallon jami’an gwamnatocin jihohi kuma muhimmin abu ne su san cewa duk motsin da suka yi ana lura da shi, kamar yadda ake kallon jami’an gwamnatin tarayya.”

Mr. Carson yace dole ne Nigeria da shugabanninta su tabattarda cewa duk abinda zasuyi, sunyi don tabattarda ganin nasarar wadanan zabukka. Me zai faru idan aka kasa?

“Idan aka kasa, ‘yan Nigeria dake da matsanancin karfin imani gameda yiyuwar wadanan zabukkan, zasu daina amincewa shugabannin nasu, da kuma ma’aikatun da shugabbanin ke jan ragamarsu.

Haka kuma mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka din, Johhnie Carson, ya jinjina wa shugaban hukumar zaben ta Nigeria, kan kokarin da yayi zuwa yanzu wajen gudanarda wadanan zabukkan – ba kamar wadanda a:

“Prof Jega, shugaban hukumar zaben, yayi jan namijin kokari wajen gudanarda shirin wannan zaben, kuma ya maido da martabar hukumar zaben wacce girmanta da kimarta sun dade da zubewa a hannun tsohon shugaban hukumar, Prof. Maurice Iwu.

XS
SM
MD
LG