Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tayi Sabon Shugaban Kasaa


Sabon Shugaban Amurka Donald Trump da dansa Barron da matarsa Melania

Zaben da aka yi jiya a nan Amurka ya bada sakamakon bazata saboda masu bin digdigin alamuran siyasa sun yi kiyasin cewa Hillary Clinton ce zata yi galaba

Bayan da alamun sakamakon zaben na nuna cewa Hillary Clinton ba zata kai labari gida ba shugaban kemfen dinta ya fito bainar jama'a ya gayawa magoya bayansu da su watse tare da cewa su ba zasu bada kai bori ya hau ba.

A jawabinsa yace zasu bi duk kuri'un da aka kada a kidayasu kakaf kafin a san wanda ya ci zabe.

Bisa ga duk alamu ita 'yar takarar Hillary Clinton ta canza shawara domin Donld Trump yace ta kirashi ta tayashi murnar nasarar da ya samu, wato ta saduda. Babu wata jayayya kuma ke nan.

Cikin jawabin da ya yiwa magoya bayansa, sabon shugaban Donald Trump ya yabawa Hillary Clinton. Ya kirata mace mai kwazo da hazaka. Yace a yaba mata saboda ayyukan da ta yiwa kasar Amurka.

Yanzu da amurkawa suka bayyanawa duniya wanda suke son ya shugabancesu, Donald Trump ya kira duk amurkawan, 'yan Republican da Democrat da kowa da kowa da a hada kai domin kasar ta cigaba. Yace shi zai zama shugaban duk amurkawa ba tare da nuna banbanci ba ko kyamar wani.

XS
SM
MD
LG