Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: 'Yan Dimokrat Sun Nemi Sessions Ya Tsame Hanunsa a Binciken Rasha


Jeff Sessions (Dama)

‘Yan Jam’iyyar Dimokrat a majalisar Dokokin Amurka, suna kira ga Babban Attorney Janar din kasar, Jeff Sessions da ya tsame hannunsa a binciken da ake yi na zargin kutsen da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar a watan Nuwamban bara, ko kuma yayi murabus daga mukaminsa.

Wannan kira da ‘yan jam’iyyar Dimokrat suka yi, na zuwa ne bayan da aka gano cewa a bara Sessions ya gana da jakadan Rasha na Amurka.

A lokacin ya na Majalisar Dattawan Amurka, Sessions ya goyi bayan shugaba Trump yayin yakin neman zabe, inda ya rike mukamin mai ba da shawara a kwamitin yakin neman zabe.

A lokacin da ‘yan majalisa suke tantance shi a bayan da shugaba Trump ya mika sunansa a matsayin wanda zai jagoranci hukumar shari’ar kasar, an tambayi Sessions ko mai zai yi idan aka samu hujjar cewa wani na hannun daman Trump ya tuntubi Rasha?

Sai ya ce: “A wani lokaci ko kuma a wasu lokuta , akan kira ni da sunan dan-baranda a yakin neman zabe, kuma ni ban yi wata ganawa da Rasha ba, Saboda haka ba zan iya cewa komai a kai ba.”

Shi dai Sessions ya taba ganawa da Jakadan Rasha Sergie Kislyak a watan Yuli a gefen babban taron jam’iyyar Republican, sannan sun sake haduwa a watan Satumba a ofishinsa dake majalisar dokokin Amurka.

Sai dai mai Magana da yawun ma’aikatar shari’ar Amurka, Sarah Isgur Flores, ta ce Sessions bai yi karya a bayanin da ya yi wa kwamitin ‘yan majalisar da suka tantance shi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG