Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Yunkurin Sake Kidaya Kuri'un Pennsylvania Ya Samu Cikas


Jill Stein

Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasa a Jami’yar Green Party a nan Amurka, Jill Stein, ta ce za ta dangana da kotun tarayya, a kokarin da ta ke yi na ganin an sake kidaya kuri’un Jihar Pennsylvania na zaben shugaban kasar da aka yi.

Stein ta janye yunkurin ta na neman a sake kidaya kuri’un na Pennsylvania ne, bayan da wani alkalin kotun jiha ya ba da umurnin ta biya kudin takardun bashi na Bond, har na dala miliyan daya.

Lauyan Stein, Jonathan Abady, ya ce sun dauki matakin zuwa kotun tarayya ne saboda kotun jihar ba ta da kwarewar da za ta saurari bukatarsu, ta sake kidaya kuri’un jihar ta Pennsylavania.

A gobe Litinin ake sa ran Stein za ta garzaya kotun tarayya domin ganin an sake kidayar.

Baya ga jihar ta Pennsylvania, Jill Stein har ila yau ta na nema a sake kidaya kuri’un juhohin Michigan da Winsconsin.

Shugaba mai jiran gado Donald Trump ya kwatanta wannan yunkuri a matsayin "aikin baban giwa" inda ana so a yi "cuta."


XS
SM
MD
LG